Jamus: Shekara guda da babban kawancen gwamnati | Siyasa | DW | 14.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus: Shekara guda da babban kawancen gwamnati

Shekara guda ke nan da babban gwamnatin kawance ke mulki a Jamus. Sai dai gwamnatin na fuskantar babban kalubale na cimma muradunta kan muhimman batutuwa na ketare.

Shekara daya da girka babban kawance na ja'miyyun siyasa a Jamus wanda ake kira da sunan Groko wanda ya ba da damar kafa gwamnatin hadaka bayan da aka kwashe watanni kafin kafuwar gwamnatin. Kawance tun farko ana yi masa kallon wani sabon yunkuri na hobasa ga Kungiyar Tarrayar Turai EU. Sai dai kuma hakan ya fuskanci kalubale a game da batun ficewar Birtaniya daga EU da kuma karuwa jam'iyyun siyasa masu ra'ayin kyamar baki a nahiyar Turai.

A karo da dama dai shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya sha yin kira ga Jamus da ta zame garkuwar nahiyar Turai ta fannin al'amura dabam-dabam da suka shafi rayuwa ral'umma da ma batun tattalin arziki da kuma na 'yan gudun hijira da tsaro. Amma a irin yanayin da ta samu kanta a ciki tun bayan zaben sabuwar shugabar jam'iyyar CDU Annegret Kramp-Karrenbauer wacce ma ake ganin nan gaba ita ce za ta kasance sabuwar shugabar gwanatin Jamus a karshen wa'adin mulkin Angela Merkel, hakan ya sa Merkel tana yin dari-dari  wajen ba da kai bori ya hau ga duk wasu bukatu na waje.

"Wata hanya ce ta dabam, sai dai kuma akwai shakku a game da cudanyar kowa, abin da yake kallo shi ne amfani da moriyar da kasarsa za ta samu. A samu wani yanayi wanda kowa zai ji ya samu yadda yake so, ina da shakku ya kamata da farko mu maida hankali ga amfanin da kasarmu za ta samu da kuma bukatun da muke da su. Ta yadda haka muke yin tunanin amfani da wasu kasashen za su samu wannan sune sharudda na farko na duk wata mu'amula da sauran kasashe."

Batun bakin haure ya mamaye manufofin Jamus dangane da Afirka

Batun bakin haure ya mamaye manufofin Jamus dangane da Afirka

Akwai dai sabani na ra'ayoyi da ake samu tsakanin Jamus din da kasashen tsakiya na nahiyar Turai da kuma na gabashi a kan batun 'yan cirani da batun tsaro da wasu sauye-sauye na tsarin tafiyar da al'amura a cikin kasashen na Turai. Misali kasashen Poland da Jamhuriyar Check da Slovakiya da Hungary na da ra'ayoyinsu da ke sabani da na Jamus a kan batun 'yan gudun hijira. Yayin da irin mulkin kama karya da ake yi Poland ke tayar wa da kawancen da ke mulki na Jamus da hankali.

A share guda hulda tsakanin Jamus da Rasha ta kasance cikin wani halin tsaka mai wuya tun bayan da Rashar ta mamaye yankin Kirimiya. Sai dai ya zama wajibi Jamus din ta kyautata huldarta da Rasha saboda iskar Gas da take saya daga Rasha ko da tana son shiga tsakani a game da rikicin da ake yi tsakanin Ukraine da Rashar to dole ne ta yi taka tsan-tsan.

Babban kawance na jam'iyyun da ke yin mulki a Jamus wato Groko manufofin da yake da su a kan Afirka shi ne na samar da hanyoyin magance kwarara bakin haure ta hanyar zuba jari a kasashen domin samar da guraben aiki ga galibi matasan da ke zuwa ci-rani, abin da ke zaman babban hadari a garesu. A fannin tsaro da sannu a hankali Jamus din na kara kasancewa a nahiyar Afirka kamar yadda ita kanta shugabar gwamnatin Angela Merkel ta bayyana a lokacin taron da aka yi a kan tsaro a birnin Munich.

''Muna a Mali muna yin kokarin yaki da ta'addanci tare da hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya muna ba da horo ga sojoji na rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar da ma sojojin Malin. Hakan ba zai yi tasiri ba ga kasar idan har ba ta da wasu muradu da ta sa a gaba na tattalin arziki. Har yanzu dai ba mu fayyace irin tsarin taimakon raya kasa ba da muka yi ba a kan kasashen Afirka za mu yi shi tare da hadin gwiwar kungiyar AU."

Kamfonin kera motoci na Jamus na tsoron wani rikicin kasuwanci da Amirka

Kamfonin kera motoci na Jamus na tsoron wani rikicin kasuwanci da Amirka

A huldar kasuwanci da gwamnatin hadakar da Jamus take yi a Amirka lamarin ya yi sanyi sakamakon take-taken da gwamnatin Donald Trump take yi na baya-baya, shi ne tuwon fashin da Amirka ta ci a game da batun yarjejeniyar nukiliya ta Iran, wacce a Berlin da kuma Brussels ake ganin wata babbar barazana da ta sa suka kara farkawa.

A bangaran yankin Asiya siyasar ta Jamus a China na tafiya duk da ma cewar China na da wasu manufofi na kasuwanci da na hakkin bil Adama da suka saba ma ka'ida. Kana wani sabon al'amari wanda ya faru a baya-baya nan shi ne na rashin tabbas da ake da shi a kan kamfanin Huawei na China, abin da zai iya gurbata huldar kasuwanci tsakanin Jamus din da China. Yayin da a cikin watan Fabrairu shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta kai ziyara a Japan. inda ta aza damba a kan wani shirin na karfafa hulda tsakanin Japan din da Kungiyar Tarayyar Turai.

Sauti da bidiyo akan labarin