Jamus na zargin Turkiyya da bai wa ′yan ta′adda mafaka | Siyasa | DW | 18.08.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jamus na zargin Turkiyya da bai wa 'yan ta'adda mafaka

Ma'aikatar cikin gida ta Jamus ta yi imanin cewar Turkiyya ta maida kanta zuwa wani dandalin aiyukan tarzoma na kungiyoyi masu matsanancin ra'ayi a Gabas ta Tsakiya da yankin Gulf.

Ma'aikatar ta ce wannan bayani yana kunshe ne cikin wani rahoto da hukumar leken asirin kasar Jamus ta gabatar, inda rahoton ya ambaci dangantakar da ke tsakanin jami'an Turkiyya da na kungiyoyin musulmi masu tsattsauran ra'ayi da kungiyoyi kamar na Hamas da 'yan uwa musulmi da sauran kungoyoyi masu dauke da makamai.

Ma'aikatar cikin gidan ta Jamus, ta ce wannan rahoton hukumar leken asirin kasar ya yi daidai da rahotannin da aka samu tun farko bayan binciken kungiyar hadin kan Turai game da matsayin kungiyar Hamas, wadda ma tun shekara ta 2003 ake kwatanta ta a matsayin kungiyar ta'adda. Bayan da kungiyar ta Hamas ta ci zabe a yankunan Falesdinawa a shekara ta 2006, kasashen Turai sun nuna matukar rashin jin dadinsu, yayin da gwamnatin Turkiyya ta jam'iyyar AKP, ta yi marhabin da wata tawaga ta Hamas a birnin Ankara. Goyon bayan Turkiyya ga kungiyar ta Hamas ya kai kololuwarsa a shekara ta 2010 lokacin da Turkiyya ta tura wani jirgin ruwa dauke da kayan agaji zuwa yankin Gaza da ke karkashin mulkin kungiyar ta Hamas, wanda Isra'ila suka kashe 'yan Turkiyya 10.

Zargin Erdogan da kokarin danne 'yan adawa


Wannan sabon sabani tsakanin Jamus da Turkiyya, yana zuwa ne a daidai lokacin da kasashen biyu suke takun saka sakamakon matakan da Turkiyya take dauka kan 'yan adawa tun bayan juyin mulkin da bai yi nasara ba a farkon watan Yulin da ya gabata.
Jamus tana zargin shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da laifin amfani da kokarin juyin mulkin domin tankade da rairaya bisa manufar kawar da 'yan adawa gaba daya daga kasar ba tare da ya kula da dokokin kasa da kasa ba. Turkiyyan tana kuma halin rashin jituwa da kasashen kungiyar hadin kan Turai kan yarjejejiyar 'yan gudun hijira. To sai dai Angela Merkel tana shan suka game da dagewar ta kan aiwatar da yarjejeniya tsakaninta da Turkiyya. Sevim Dagdelen daga jam'iyyar Linke ta masu neman canji ya ce:

"Shugabar gwamnati Angela Merkel tilas ne ta yanke shawarar da ta dace, domin kuwa ba zai yiwu a sami hadin kai da kasar da ke goyon bayan aiyukan tarzoma ba. Ba zai yiwu a sami wani hadin kai da gwamnatin da ke taimaka wa kungiyoyi masu matsanancin ra'ayi a Gabas ta Tsakiya da yankin Gulf ba da kuma basu dandalin da za su rika tafiyar da aiyukansu."
Manufofin Merkel kan Turkiyya na shan suka

A bayan da ma'aikatar cikin gidan ta Jamus ta fitar da rahoton goyon bayan da Turkiyya take bai wa kungiyoyi na tarzoma, masu sukan manufofin Angela Merkel kan Turkiyya, sun yi zargin cewar wadannan manufofi na Merkel sun saba wa irin yadda Turkiyyan take a zahiri saboda haka wajibi shugabar gwamnatin ta Jamus ta yi karatun ta nutsu. A dayan bangaren Jamus na matukar bukatar Turkiyya a yakin da kasashen yamma suke yi kan kungiyar IS da kuma samun nasarar manufofinta na 'yan gudun hijira. Kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Jamus Sawsan Chebli da take jawabi ga manema labarai a birnin Berlin game da rahoton hukumar leken asirin Jamus ta ce:

"Mu a ma'aikatar harkokin waje, abin da zan iya shaida maku shi ne, ba za mu dauki wadannan rahotanni da ke ta yawo a kafofin yada labarai mu maida shi ya zama na mu ba."

Ya zuwa yanzu dai kungiyar NATO, wadda Turkiyya take daya daga cikin wakilanta, ba ta yi wani sharhi ba game da rahoton da ma'aikatar cikin gidan Jamus ta gabatar.

Sauti da bidiyo akan labarin