Jamus da Faransa sun ce a mutunta yarjejeiyar Ukraine | Labarai | DW | 28.08.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus da Faransa sun ce a mutunta yarjejeiyar Ukraine

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa, sun yi kira ga kasar Rasha da ta kara kaimin ganin yarjejeniyar tsakaiga wuta a gabashin kasar Ukraine ta tabbata.

Shugabannin biyu sun ce suna matukar damuwa da halin tabarbrewar da al'amura ke yi a gabashin na Ukraine, a saboda haka ne suke bada hankali kan lamarin da ke faruwa. Sun gana ta waya kai tsaye da shugaba Putin na Rasha da ma Petro Poroshenko na kasar Ukraine dangane da matsalar. Yarjejeniyar da jagororin manyan kasashen biyu ke batu a kanta dai, yarjejeniya ce da aka sanya wa hannu a shekara ta 2015 a garin Minsk, babban birnin kasar Belarus. Akalla dai mutane dubu 10 ne suka salwanta a yakin da ake kafsawa a gabashin kasar ta Ukraine.