Hukumar FIFA ta dakatar da Jami′an ta biyu | Labarai | DW | 21.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar FIFA ta dakatar da Jami'an ta biyu

Hukumar ta FIFA ta dakatar Amos Adamu da Reynold Tamarii bisa zargin cin hanci da rashawa.

default

Daga hagu Amos Adamu sai kuma Reynald Tamarii a dama

Hukumar wasan kwallon kafa ta duniya FIFA ta da dakatar da biyu daga cikin mambobin kwamitin ta dangane da sarƙaƙiyar sayar da ƙuriun su, na ƙasar da zata karɓi baƙunci gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya a shekarar 2018 da 2022 da aka gano.

Idan dai ba'a manta ba, a makon da ya gabata ne, wata jaridar Birtaniya ta bankaɗo yunƙurin jami'an biyu na FIFA waɗanda suka haɗa da Amos Adamu ɗan Najeriya da Reynald Temarii daga Tahiti na neman toshiyar baki na zunzuruntun kuɗi kafin su kaɗa ƙuri'a ga dukkan ƙasar da ke son ɗaukan baƙuncin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na duniya shekarar 2018.

A halin da ake ciki, Kwamitin tabbatar da ɗa'a ta FIFA ya dakatar da jami'an biyu, na tsawon kwanaki talatin, domin gudanar da cikakken bincike, bugu da ƙari mambobin biyu ba za su iya kowace irin hidima ta ƙwallon ƙafa ba, har sai kwamitin binciken ya kammala aikin sa.

Ana dai sa ran gudanar da zaɓen ƙasar da za ta karɓi baƙuncin gasar cin kofin ƙwallon kafa ta duniyan na shekarar 2018 da 2022 a ranar biyu ga watan Disamban bana.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Abdullahi Tanko Bala