UEFA kungiyar kula da wasan kwallon kafa ta kasashen Turai, wadda take daya daga cikin kungiyoyin nahiyoyi shida na duniya na kwallon kafa.
Kungiyar tana da mambobi 54, inda take shirya gasa gami da bayar da damar nunawa ta kafofin yada labarai. Ita take shirya gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai da kuma gasar neman cin kofin kwallon kafa na nahiyar ta Turai.