Gwamnatin wucin gadi tace zata kafa dokar ta baci a Somalia | Labarai | DW | 29.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Gwamnatin wucin gadi tace zata kafa dokar ta baci a Somalia

Firaministan kasar Somalia Ali Muhammad Gedi yace majalisar dokokin kasar zata aiyana dokar tabaci don tabbatar da doka da oda a kasar.

Wannan kuwa ya biyo bayan kwace babban birnin kasar ne Mogadishu da dakarun gwamnati dana Habsaha sukyi daga hannun kotunan musulunci na kasar.

Bayan kwanaki 10 na fafatawa tsakanin dakarun kotunan musulunci da na gwamnatin dakarun masu goyon bayan Habasha sun samu shiga muhimman wurare da magoya bayan kotunan na muslunci suke rike da shi.

A nasu bangare membobin kungiyar ta islama sunce sun janye ne domin kaddamar da yakin sunkuru da nufin korar dakarun Habasha daga Somalia.

A halinda ake ciki kuma wasu manyan malami 14 daga Saudiya sun zargi Amurka da laifin taaddanci saboda goyon bayanta ga mamayar da Habasha tayiwa Somalia.

Sun kuma yi Allah wadai da manyan kungiyoyin kasa da kasa kamar MDD game da shiru da sukayi game da abinda suka kira aiyukan taadanci akan Somalia.