Dangantaka ta kara yi tsami tsakanin Pakistan da Indiya | Labarai | DW | 05.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dangantaka ta kara yi tsami tsakanin Pakistan da Indiya

Pakistan da Indiya sun ba da umarnin korar jami´o´in diplomasiya kowace daga cikin su daga kasashen biyu. Da farko Pakistan ta bukaci Indiya da ta janye jami´in diplomasiyanta Deepak Kaul daga birnin Islamabad. Wani kakakin ma´aikatar harkokin wajen Pakistan ya ce jami´in na tafiyar da aikin leken asiri a Pakistan. Jim kadan bayan haka Indiya ta mayar da martani, inda ma´aikatar harkokin wajen ta ta umarci wani dan diplomasiyan Pakistan da ya fice daga kasar ba tare da ta ba da dalilin yin haka ba. Dangantaka tsakanin kasashen biyu ta kara yin tsami tun bayan hare haren bam da aka kai kan jiragen kasa na birnin Bombay.