Kashmir yanki ne da ke tsakanin Indiya da kasar Pakistan wadda kasashen biyu suka shafe shekaru da dama suna rikici dangane da mallakarsa.
Tun a cikin shekarar 1947 ne kasashen biyu ke rikici kan yankin na Kashmir da ke da yawan tsaunuka. Yanzu haka dai yankin na da yawan al'umma da suka haura miliyan 16.