Pakistan kasa ce da ke yankin kudancin Asiya wacce ta balle daga Indiya a shekarar 1947. Islamabad ne babban birninta, kuma akasarin 'yar kasar Musulmi ne.
Kasar tarraya ce da ta kunshi jihohi hudu. Pakistan ce kasa ta biyu da ta fi yawan Musulmi a duniya. Bayan samun 'yancin kanta ta yi fama da juye-juyen mulkin soji. Sau uku ta gwabza yaki da makwabciyarta Indiya.