1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Shehbaz Sharif zai zama firaministan Pakistan na gaba

Suleiman Babayo AH
February 21, 2024

Manyan jam'iyyun siyasa biyu na kasar Pakistan da suka samu rinjayen kuri'u a zaben da ya gabata sun amince da kafa gwamnatin kawance domin shawo kan rikicin siyasa da kasra ke fuskanta.

https://p.dw.com/p/4ciCv
Pakistan, Lahore | Shehbaz Sharif
Shehbaz Sharif wanda zai zama firaministan Pakistan na gabaHoto: K.M. Chaudary/AP/picture alliance

Karkashin tsarin jam'iyyar PML-N ta tsohon Firaminista Nawaz Sharif za ta kawo firamnista sannan jam'iyyar PPP ta Bilawal Bhutto Zardari za ta bayar da goyon bayan kafa gwamnati, inda aka amince da dan-uwan tsohon firaministan wanda shi kansa tsohon firaminista ne, Shehbaz Sharif a matsayin wanda zai jagoranci gwamnatin ta gaba bisa mukamun firaminista.

Sai dai jam'iyyar PPP ba za ta karbi wani mukami ba, amma za ta rika duba manufofin gwamnatin wajen bayar da goyon baya. Zaben da aka gudanar ranar 8 ga wannan wata na Febrairu a kasar ta Pakistan ya kare ba tare da an samu jam'iyyar da ta samu rinjayen da aka bukata ba wajen kafa gwamnati kai tsaye.

Tuni tsohon Firaminista Imran Khan wanda yake garkame a gidan fursuna kuma magoya bayan sa suka shiga zaben a matsayin 'yan takara masu zama kansu, saboda haramta wa jam'iyyarsa, ya yi tir da matakin manyan jam'iyyun na kafa gwamnatin kasar ta Pakistan ta gaba.