1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Damar amfani da fasfuna biyu a Jamus

April 8, 2014

Majalisar ministocin Jamus ta amince da sassauta tsauraran matakan ta kan 'ya'ya bakin da aka haifa kasar da ke son amfani da fasfon kasar da na kasarsu ta asali.

https://p.dw.com/p/1BdsX
Doppelte Staatsbürgerschaft
Hoto: picture-alliance/dpa

Cikin kunshin daftarin dokar da suka amince da ita, dukkanin 'ya'yan bakin da suka kai shekaru 21 ko kuma suka zauna kasar na tsawo shekaru 8 ko suka hallarci makaranta a Jamus din na shekaru 6 suna da 'yancin amfani da fasfon Jamus.

Gabannin amincewa da dafarin wannan doka dai, 'ya'yan bakin da ke tarayyar ta Jamus na da zabi daya ne game batun daukar fasfo, walau na asalin kasar da iyayensu suka fito ko kuma na tarayyar ta Jamus kuma sai sun kai shekaru 23 ne kawai za su iya yin haka.

Nan da 'yan watanni masu zuwa ne dai majalisar dokokin Jamus ta Bundestag za ta duba wannan doka da nufin amincewa da ita, yayin da a hannu guda Turkawa da suke zaune a Jamus wanda ake ganin 'ya'yansu za su fi kowa amfana daga tsarin suka fara kokawa game da sarkakakiyar da ke kunshe da lamarin.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman