1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram: Muhammadu Buhari ya kai ziyara Nijar

Abddoulaye Mammane Amadou/ASJune 3, 2015

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara Nijar don tattaunawa kan kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta da nufin kawo karshen matsalar a kasar da makotanta.

https://p.dw.com/p/1FbKo
Nigeria Bildergalerie Staatspräsidenten Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Akinleye

Ziyarar ta Shugaba Buhari a Jamhuriyar ta Nijar dai ta maida hankali ne kan tattaunawa da mahukuntan kasar kan batutuwa da dama da suka jibanci tattalin arzikin kasashen biyu da kuma kara kayautata huldar da ke tsakan kanin kasashen, baya ga hakan batun tsaro musamman ma yaki da kungiyar Boko Haram da ke addabar kasashen biyu na daga cikin mahimman batutuwan da shugabannin kasashen biyu suka zanta a kai.

Shugaba Buharin dai ya isa Nijar din ne da tawagar da ta kunshi kwararru ta kowane fanni da suka shafi batutuwan tsaro da tattalin arzika da inganta huldar kut da kut da ke tsakanin kasashen biyu domin tattaunawa da takwarorinsu na Jamhuriyar Nijer.

Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Rikicin Boko Haram na daga cikin batutuwan da ke ci wa Najeriya da Nijar tuwo a kwarya.Hoto: Reuters/Emmanuel Braun

Da ya ke tsokaci kan wannan ziyara, Garba Shehu babban mai taimakawa shugaban kasar ta Najeriya a fannin sadarwa ya ce ''sabon shugaban Najeriya ya na da niyar yin gyara ga abinda ya lalace a baya saboda hakan muna tafe da kwararru kala-kala:'' Shi kuwa Professeur Ado Mahaman Malami ne a fannin tarihi kuma shugaban jami’ar Tahoua na ganin cewar ''ziyarar ta Muhammadu Buhar na da ma’ana sosai ganin irin kalubalen da ke gaban kasashen da ke yankin tabkin Chadi.''

Nigeria Erfolge der Offensive im Kampf gegen Boko Haram
Jamhuriyar Nijar na daga cikin kasashen da ke makotaka da Najeriya da ke dafawa kasar wajen magance kalubalen tsaro.Hoto: F. Batiche/AFP/Getty Images

Daukacin titunan birnin Yamai dai sun kasance a cikin yanayi na kwalliya da tutocin kasashen Najeriya da Nijer baya ga allunan barka da zuwa ga shugaban inda wasu ke dauke da sakonnin taya murna gare shi, a hannu guda kuwa kungiyoyin fararen hula sun yi shelar fita don tarbarsa, kiran da mutane da dama suka amsa shi yadda ya kamata.