Austreliya ta ce ta sami rahotannin kungiyar leken asiri da ke nuna cewa `yan ta’adda na shirin kai mata hari a cikin kasar. | Labarai | DW | 02.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Austreliya ta ce ta sami rahotannin kungiyar leken asiri da ke nuna cewa `yan ta’adda na shirin kai mata hari a cikin kasar.

2. Austreliya ta ce ta sami rahotannin kungiyar leken asiri da ke nuna cewa `yan ta’adda na shirin kai mata hari a cikin kasar.

Firamiyan kasar Austrreliya, John Howard, ya ce jami’an tsaron kasar sun sami rahotannin leken asirin da ke nuna cewa, ana shirn kai wa kasarsa harin `yan ta’adda. Firamiyan ya bayyana hakan ne a wani taron maneman labarai a birnin Canberra, amma bai ba da karin bayani kan rahoton barazanar harin ba, wanda ya ce a cikin wannan makon ne jami’an tsaron suka samu.

Sanarwar John Howard din dai ta zo ne a daidai lokacin da gwamnatinsa ke kokarin gabatad da wata dokar yaki da ta’addanci ga majalisar kasar, wadda kuma take son ganin an zartar kafin kirismeti. Kawo yanzu dai, ba a taba kai wani mummunan hari a cikin Austreliya din ba. Amma an sha afka wa `yan kasar da kuma ofisoshin diplomasiyyarta a ketare, da harin bamabamai, musamman ma dai a kwanakin bayan nan a kasar Indonesiya.