Australiya ta ce likitan nan na Indiya Haneef ka iya barin kasar | Labarai | DW | 28.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Australiya ta ce likitan nan na Indiya Haneef ka iya barin kasar

An amince likitan nan dan kasar Indiyan wanda hukumomin Australiya suka tsare shi dangane da alakar sa da shirin kai hare haren bama-bamai a Birtaniyya da ya bar kasar ta Australiya. Ministan kula da shige da ficen baki na Australiya Ken Andrews ya ba da wannan sanarwa a lokacin da yake magana da manema labarai.

Andrews:

“Bayan na karbi shawarwari musamman daga hukumar ´yan sandan tarayyar Australiya, ina mai sanar da cewa Komonwelf ba zata yi adawa da ficewar Hanif daga Australiya ba. Dalilin day a sa aka janye izinin sa na zama cikin wannan kasa shi ne don ya gaggauta ficewa.”

A jiya juma´a aka fid da Mohammed Haneef daga kurkuku bayan an janye tuhumar da ake masa. To sai dai da farko gwamnati ta ce ba zai iya barin kasar ba.