Angela Merkel tayi Allah wadai da hukunci da kotun Libya ta zartar. | Labarai | DW | 19.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Angela Merkel tayi Allah wadai da hukunci da kotun Libya ta zartar.

Alkawarin kasashen G8 ga Nahiyar Afrika

Alkawarin kasashen G8 ga Nahiyar Afrika

Shugabar gwamnatin jamus Angela Merkel tayi Allah wadai da hukuncin kisa da aka yankewa wasu maaikatan jiyya su 5 yan kasar Bulgaria da wani likita Bapalasdine,saboda laifi da aka kama su da shi na yiwa wasu yaran Libya 400 allurar kamuwa da kwayar cutar kanjamau.

A wani labarin kuma,ministan harkokin wajen kasar Jamus Frank Walter Steinmeire yace gwamnatin kasar zata maida hankalinta ne kan kundin tsarin mulkin kungiyar taraiyar turai a lokacinda kasar zata karbi shugabancin kungiyar daga ranar 1 ga watan janairu mai kamawa.

Steinmeire ya baiyanawa manema labarai shirin na Jamus yana mai fadin cewa sake yin gyare gyare cikin kungiyar zai sake maido da martabarta.

Yace shugabancin Jamus a kungiyar zai kuma taimaka wajen magance manyan kalubale kamar rikicin kasar Iraqi da kuma tsakanin Israila da Plasdinawa.