ANC ta lashe zaben Afirka ta Kudu | Labarai | DW | 10.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

ANC ta lashe zaben Afirka ta Kudu

Hukumar zaben Afirka ta Kudu ta ce jam'iyyar African National Congress wato ANC ta shugaba Jacob Zuma ta lashe zabukan da aka yi a kasar a ranar Larabar da ta gabata.

Bisa ga kuri'un da aka kada a mazabu dubu 22 da ke fadin kasar inji hukumar, jam'iyyar ANC ta samu kashi 62 cikin 100, yayin da jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance ko DA a takaice ta samu kashi 22 cikin 100.

Da ya ke jawabi ga al'ummar kasar bayan bayyana sakamakon zaben a hukumance, shugaba Jacob Zuma ya ce nasarar da jam'iyyarsa ta ANC ta samu nasara ce ta al'umma kuma wata 'yar manuniya ce ta irin shaukin da al'ummar kasar ke da shi na son ganin ANC din ta cigaba da bunkasa tattalin arzikin kasar da samawa al'umma aiyyukan yi.

Wannan dai shi ne karo na hudu da aka gudanar da zabe makamancin wannan tun bayan da aka kawar da mulkin wariyar launnin fata a Afirka ta Kudun kimanin shekaru 20 din da suka gabata.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal