1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sace motoci 20 na hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Dunia a yankin Darfur

February 7, 2006
https://p.dw.com/p/Bv94

Hukumar Majalisar Dinkin Dunia mai kulla da bada taimakon abinci, ta nuna damuwa a game da halin da jami´an ta ke ciki a yankin Darhur na kasar Sudan.

Kakakin wannan hukuma, ya bayyana cewa a satin da ya gabata, mutane dauke da makamai sun yi awan gaba, da motoci a kalla 20 mallakar hukumar .

A halin yanzu a cewar sa, hukumar na tallafawa mutane kussan million 3 da abinci,a yankin Darfur, amma a kawai alamun dakatar da talafin, idan a ka cigaba da fuskantar tabarbarewar matakan tsaro.

Shugabanin hukumar, sun tuntunbi magabatan yan tawayen Darfu,r da na gwamnatin Sudan , amma har yanzu babu wani mataki da su ka dauka a kai.