Amnisty ta zargi China, da rura wutar rikici a dunia.
June 12, 2006Hukumar kare haƙƙoƙin bani adama ta dunia,wato Amnisty International, ta bayana rahoto a game da ƙasar China.
Rahoton yayi matuƙar suka ga wannan ƙasa, da cewar, itace ke hadasa rikici, a yankuna masu yawa, na dunia, ta hanyar sayar da makamai.
Amnisty ta ɗora alhakin yaƙe- yaƙen da ke wakana,
a ƙasashen Sudan, Nepal, da Birmanie a kan hukumomin Sin.
Shugaban hukumar yaƙi da cinakin makamai ,na Amnisty International, Helen Hughes, ya ce a duk shekara ta Allah, kasar Sin, na sayar da makamai na fiye da dalla billiard daya.
Sannan, binciken da su ka gudanar, ya tabatar da cewa, a watan mayu na shekara ta 2005, China ta aika motocin yaƙi masu sulke,200, a ƙasar Sudan.
Cemma, a rahoton ta na shekara shekara, hukumar ta kare haƙƙoƙin jama´a, ta jera China, a sahun ƙasashen da su ka yi ƙaurin suna, ta fannin tozarta bil adama.