Ƙungiyar EU akan Rikicin Gabas ta Tsakiya | Siyasa | DW | 08.01.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ƙungiyar EU akan Rikicin Gabas ta Tsakiya

A cigaba da laluɓo hanyar sasanta rikicin Israela da Palatsinawa, a yau ƙungiyar tarrayar turai ta fitar da sanarwar cewa zata sake maida hukumar kungiyar dake sa'ido a yankin Rafah.

default

Rugujewar gini a Rafah (AP Photo/Eyad Baba)

A cigaba da laluɓo hanyar sasanta rikicin Israela da Palatsinawa, a yau ƙungiyar tarrayar turai ta fitar da sanarwar cewa zata sake maida hukumar kungiyar dake sa'ido a yankin Rafah dake iyakar Gaza da Kasar Masar. Yankin da Israela ke zargin ƙungiyar Hamas na anfani dashi wajen shigar da makamai izuwa Gaza.

Dama dai ƙungiyar EU tana da hukumar dake zaune a wannan yankin amma an janye tane bayan da ƙungiyar Hamas ta karɓi iko da yankin Gaza a shekara ta 2007. Wannan jawabin ya fito ne daga bakin shugaban kula da tsare tsaren harkokin waje na ƙungiyar ta EU Jabiya Solana, wanda yace yanzu haka wannan hukumar tannan a yankin abinda take jira shine ayi mata kwas kwarima. Jami'in na EU yana maganane a ƙasar Turkiya yayin wata tattaunawa da yayi tareda shugaban ƙasar Abdullah Gul da kuma piraiministan ƙasar Recep Tayyip Erdogan. Ƙasar Turkiya dai itace kan gaba wajen kai kawo na ganin wannan tashin hankalin yazo ƙarshe. Har ila yau ƙasar ta Turkiya itace ƙasar musulmai da take ɗasawa da Israla wanda ta fito tayi Allah wadai da kasar yahudawan bisa zubar da jinin bayin Allah da takeyi. Ita ma kungiyar kare hakkin yan jaridu ta Reporter without Bonder tayai suka bisa hana yan jaridu yancin gudanar da aikinsu wanda Israela tayi, kamar yadda jami'ar kungiyar Elke Schäfter ta bayyana wata hira da tayi da manema labarai:

"Muna adawa da duk abinda ke hana yan jaridu yancin bada rohotonnin kan abinda ke faruwa, kuma wannan ya shafi kowa walau Israela ce, Amirka ce. Wannan bazai taimaka mba kuma bazai taba zama hallatace ba".


Ƙasashen duniya sunyi gom da bakinsu kan hana yan jaridu shiga Gaza da Israela tayi, ko mi kungiyar ke sonyi don ganin Israela tabi Ka'idojin duniya na barin dan jarida yayi aikinsa.


Schäfter ta ci-gaba da cewa:

"Bazan iya cewa komai ba. Domin ban fahimci dalilin yin hakan ba, ina tunanin dolene a ƙara mazin lamba koda kuwa daga gwamanatin dake a Berlin"


Yanzu haka dai ƙasar Jamus da Amurka sun yi maraba da shirin da shugaban kasar Masar Husni Mubarak da takwaransa na Faransa suka gabatar. Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeier ya baiyana gamsuwarsa ga aniyar Isra'ila ta bada dama na kai kayan agaji. A ranar Laraba komitin sulhu na MDD ya sake gagara amincewa akan yadda za a kawo karshen yaƙi a Gaza. Har yanzu membobin komitin sun kasance kawunansu a rabe bayan wakilan larabawa sun haƙikance kan batun tsagaita wuta nan take yayin da Amurka da Burtaniya da Faransa suka yi kira da bada tabbacin kare sumogan makamai ga ƙungiyar Hamas.

Usman Shehu Usman/ATL