Ziyarar shugabar gwmnatin Jamus a Biritaniya | Labarai | DW | 24.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyarar shugabar gwmnatin Jamus a Biritaniya

Aci gaba da ziyarar aiki da take , a yanzu haka shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na kasar Biritaniya don saduwa da takwaran ta wato,Tony Blair.

Babbar ajanda da shugabannin biyu zasu fi mayar da hankali kai a lokacin ganawar tasu zata shafi batun sabani ne da aka samu a kasafin kudi na kungiyyar tarayyar Turai, wato Eu.

Kafin dai isar tata kasar ta Biritaniya a jiya ,Angela Merkel ta kai irin wannan ziyara izuwa kasar Faransa a inda ta sadu da shugaba Jack Chirac.