1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zelensky zai gana da shugabannin EU kan Rasha

Abdul-raheem Hassan
December 8, 2025

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky zai gana da shugabannin kasashen Tarayyar Turai a birnin London, inda za su tattauna kan shawarwarin da Shugaba Trump ya gabatar na kawo karshen yakin Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/54vIY
Shuagban Ukraine Volodymyr Zelensky da Firaiministan Britaniya Keir Starmer da Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shuagban Ukraine Volodymyr Zelensky da Firaiministan Britaniya Keir Starmer da Shugaban Faransa Emmanuel MacronHoto: JUSTIN TALLIS/AFP

Ganawar da shugabannin za su yi, na zuwa ne bayan da Shugaba Donald Trump na Amurka ya zargi Shugaba Zelensky na Ukraine da kin karanta shawarawarin da ya gabatar na kawo karshen yakin akalla shekaru uku da Rasha.

Shugaba Zelensky zai hadu da Firaiministan Birtaniya Keir Starmer da Shugabar gwamnatin Jamus Friedrich Merz da Shugaban Faransa Emmanuel Macron don tattaunawa matsaya kan daftarin Shugaba Trump kan yakin Ukraine.

Hakan na zuwa ne bayan shafe kwanaki na tattaunawa tsakanin jami'an Ukraine da na Amurka a Miami ba tare da wata matsala ba, inda Zelensky ya yi alkawarin yin duba na tsanaki kan shawarwarin da ke cikin daftarin.