1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan gudun hijira na cikin kunci a Afirka ta Tsakiya

January 4, 2014

Yawan mazauna birnin Bangui dake tsere wa tashin hankalin da ake fama da shi a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya karu suna kuma cikin mawuyacin hali.

https://p.dw.com/p/1AlEs
Zentralafrikanische Republik Elend
Hoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai iyaka da Sudan ta kudu, hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa aƙalla mutane miliyan daya suka tsere daga gidajensu sakamakon rikicin da ƙasar ke fama da shi. Kakakin hukumar Babar Baloch ya ce daga Bangui babban birnin ƙasar kawai wadanda suka bar gidajensu sun kai mutane dubu dari biyar, wato kusan rabin mazauna birnin kenan. Kakakin ya kara da cewa tashin hankali ya sa wadanda suka fake a kusa da filin jirgin saman, a yanzu sun ruɓanya. Ya ce tashin hankali da hare-haren da ake kai wa fararen hula na kawo cikas wajen raba kayan agaji, don haka jami'in ya yi kira ga dakarun ƙasashen waje da suka je ƙasar da su yi aikin da ya kaisu don tabbatar tsaro ta yadda za a agaza wa mabuƙata.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal