′Yan Boko Haram sun kai hari Damasak | Labarai | DW | 24.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Boko Haram sun kai hari Damasak

Mutane da dama ne suka rasu sanadiyyar wani hari da wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kai garin Damasak na jihar Bornon Najeriya.

Wakilinmu Al-Amin Sulaiman Muhammad ya ce bayanai da ke fitowa daga wasu mazauna garin da suke tsira sun nuna cewa ‘yan bindigar masu yawan gaske cikin motoci da babura dauke da manyan makamai sun afkawa garin a dai dai lokacin da ake cin kasuwa inda suka yi ta harbi irin na kan mai tsautsayi.

Yanzu haka dai wasu al'ummar garin na ta tsere zuwa ga tudun na tsira ganin babu jami'an tsaro da suka kai musu dauki. Ya zuwa yanzu dai hukumomi ba su ce komai kan wannan harin ba.