Yajin aikin jiragen kasa a Jamus | Labarai | DW | 11.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yajin aikin jiragen kasa a Jamus

Kungiyar matuka manyan jiragen kasa na pasinja a nan tarayyar jamus,zasu gudanar da yajin aiki na yini guda a gobe juma’a,idan allah ya kaimu.Yajin aikin wanda zai fara daga karfe 2 na tsakar daren yau zuwa sha biyun daren gobe,yajin aikin dake zama na biyun irinsa da kungiyar Direbobin ta GDP mai wakilai dubu 34,ta gudanar a tsukin makonni da suka gabata,kamar yadda shugaban kungiyar Manfred Schnell yayi karin haske akai...

"Yace Daga misalin karfe biyu na safiyar gobe ne zamu fara wannan yajin aiki,wanda zai shafi dukkannin manyan jiragen kasa,masu tafiyar dogo da gajeren zango,wannan shine mataki da zamu dauka.daga karfe biyu zuwa 12 dare"

A ranar juma’ar data gabata nedai aka gudanar da yajin aiki makamancin wannan,wanda ya jefa pasinjoji sama da million 10 dake amfani da jiragen domin zirga zirga,cikin hali mawuyaci.