Wata tawagar Hamas ta tafi Syria don ganawa da shugaban kungiyar | Labarai | DW | 02.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wata tawagar Hamas ta tafi Syria don ganawa da shugaban kungiyar

Wata tawagar mutane uku ta kungiyar Hamas wadda talashe zaben palasdinawa ta isa kasar Syria a wata ziyara da ta fara don ganawa da shugabanta na siayasa Khaled Me shaal wanda ke zaman gudun hijira a sham din.

Wakilin kungiyar a Lebanon Osama Hamdebn yace a lokacin ziyarar jamian kungiyar zasu tattauna da shugabannasu akan batun ziyarce ziyarcen da tawagar Hmas din zata yi zuwa kasashen larabawa don bayyana matsayin kungiyar akan takaddamar da ke tsakaninta da hukumomi da sauran kasashen ,duniya masu gindaya mata sharadin watsi da manufofinta akan Israela.

Hamas din dai ta sake watsi da kiran da ake mata na yin maslaha da kuma amincewa da yancin kasar Israealabyanda a jiya shugaban hukumar leken asiri na masar omar suleman bayan wata ganawa tsakanin shugaban palasdiwa Mamud Abas da shugaban masar din Husni Mubarak