Siriya ta fada cikin yakin basasa tun shekara ta 2011, bayan da guguwar neman sauyi ta kada a wasu kasashen Larabawa.
Tun bayan da shugaba Bashar al-Assad ya yi yunkurin murkushe masu adawa da manufofin gwamnatinsa ne Siriya ta dare gida biyu. Wani bangare na kasar na hannun masu kaifin kishin addini na IS, lamarin da ya sa wasu 'yan kasar kaurace wa matsugunansu.