Wani daftarin kuduri yayi zargin keta hakkin dan Adam a Koriya Ta Arewa | Labarai | DW | 18.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Wani daftarin kuduri yayi zargin keta hakkin dan Adam a Koriya Ta Arewa

A karon farko wani kwamitin babbar mashawartar MDD ya amince da wani daftarin kuduri wanda ya zargi KTA da keta hakkin ´yan Adam wato kamar kwadagon tilas a cikin kasar ta. Daftarin kudurin ya kuma nuna damuwa game da matsalar karancin abinci a kasar musamman ga kananan yara wadanda ba sa samun abinci mai gina jiki. Daftarin kudurin wanda KTT ta gabatar ya samu goyon bayan kasashe 84, 22 sun nuna adawa yayin da 62 suka yi rowar kuri´un su ciki kuwa har da KTK. Kudurin ya yi kira ga gwamnatin birnin Pyongyang da ta girmama hakkin ´yan Adam. Za´a mika wannan daftarin kuduri ga babbar mashawartar don kada kuri´a ta karshe akai.