1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine za ta nemi zama membar EU a shekarar 2020

Mohammad Nasiru AwalSeptember 25, 2014

Shugaba Poroshenko na Ukraine ya ce nan da shekaru shida masu zuwa kasarsa za ta nemi shiga kungiyar tarayyar Turai a matsayin cikakkiyar memba.

https://p.dw.com/p/1DL4d
Petro Poroschenko 25.09.2014 Kiew
Hoto: Reuters/Valentyn Ogirenko

Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya ce zai gabatar da wani gagarumin tsarin yin gyara ga zamantakewar al'umma da tattalin arzikin kasar, wanda zai ba ta damar neman shiga kungiyar tarayyar Turai EU a cikin shekaru shida masu zuwa. A ranar 16 ga watan nan na Satumba majalisar dokokin Ukraine ta sanya hannu kan yarjejeniyar kyautata hulda da EU, sai dai an jinginar da batun aiwatar da bangaren ciniki na yarjejeniyar har zuwa watan Janerun 2016, don dadada wa Rasha, wadda ta ce shirin zai yi wa kasuwanninta illa. Poroshenko ya kuma ce a karon farko cikin watanni da yawa ba a samu rahoton mutuwa ko jikkata ba a cikin sa'o'i 24 da suka wuce a rikicin da ake da 'yan aware magoya bayan Rasha a gabashin Ukraine. Ya ce hakan na nuni da cewa shirin tsagaita wuta da aka kulla a ranar 5 ga watan Satumba ya fara aiki gadan-gadan.