Turkiya tayi tayin shiga tsakani a rikicin yankin gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 27.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Turkiya tayi tayin shiga tsakani a rikicin yankin gabas ta tsakiya

Kasar Turkiya tayi tayin shiga tsakani a rikicin Palasdinawa da Israila,bayan da kungiyar Hamas ta samu rinjaye a zaben yankin.

Firaministan Turkiya Recep Tayib Erdogan yace, mai yiwu ne kuma kungiyar kasashen musulmi ta duniya zata iya taka muhimmiyar rawa a wannan fanni .

Erdogan yayi kira ga kungiyar Hamas din data amince da kasancewar kasar Israila,ta mika makamanta ga jamian tsaron na Palasdinu ta kuma sassauto daga tsatsauran raayi da take da su na islama.

Shugaban na Turkiya ya kuma bukaci kasar Israila data amince da sakamakon wannan zabe da kuma rawa da Hamas zata taka cikin sabuwar gwamnatin Palasdinu.

Wajen taron kasashen duniya akan tattalin arzikin duniya,Erdowan yace kasarsa tana da kyakyawar dangantaka da kasashen biyu kuma yana fata Turkiya zata iya taka rawa wajen sasanta su.