1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashar nukiliya ta Fukushima na fuskantar haɗari

March 22, 2011

Jami'ai a Japan na ta ƙoƙarin shawo kan tashar nukiliyar Fukushima yayin da a waje guda ake ci gaba da fuskantar gagarumin ƙalubale

https://p.dw.com/p/10fUQ
Tashar nukiliyar Fukushima a JapanHoto: AP

Tashar nukuliyar Fukushima ta ƙasar Japan na cigaba da fuskantar babbar barazana. Wani jami'i na cibiyar kula da tashar makamashin nukiliyar yace akwai yiwuwar za'a sami ƙaruwar tiriri fiye da ƙima dake fita daga tashar nukiliyar, yana mai cewa tukwanen dake adana sunduƙan makamashin da aka riga aka ƙona sun yi tsananin zafi. Jami'in ya ƙara da cewa suna kyautata tsammanin tiririn tafasashen ruwa dake tasowa daga cikin tukwanne shi ya haifar da hayaƙin dake fita a ɗaya daga cikin cibiyoyin nukiliyar tun daga jiya Litinin har ya zuwa yau Talata. Yace idan ruwan dake cikin tankin sanyaya sunduƙan ya ƙone to akwai yiwuwar za'a sami ƙarin yaɗuwar tiririn. Tuni dai gwamanatin Japan ɗin ta gargaɗi da jama'ar dake zaune a kusa da tashar nukiliyar cewa kada su sha ruwa famfo.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi