Taron tantance makomar Tarayyar Turai | Labarai | DW | 25.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron tantance makomar Tarayyar Turai

Kasashen da suka jagoranci kafa Tarayyar Turai suna taro a Jamus bayan kuri'ar raba gardama da ta janyo ficewar Birtaniya daga kungiyar.

Kasashen da suka kafa Tarayyar Turai suna taro a birnin Berlin na nan Jamus a wannan Asabar, domin duba makomar kungiyar bayan kuri'ar da Birtaniya ta kada na ficewa daga cikin kungiyar.

Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier zai karbi bakoncin na Faransa, da Holland, da Italiya, da Belgiyam, da kuma Luxemburg da suka jagoranci kafa kungiyar. Tuni Tarayyar Turai ta nemi fara tattaunawa kan ficewar Birtaniya cikin hanzari ba tare da jira sai Firaministan Birtaniya David Cameron ya ajiye madafun iko ba cikin watan Oktoba mai zuwa.

A wani labarin kuma Shugaba Barack Obama na Amirka ya tabbatar da cewa kasar za ta ci gaba da dangantaka ta musamman da Birtaniya, duk da kuri'ar raba gardama da ta kawo karshen Birtaniya cikin kungiyar kasashen Turai.