Taron ministoci a Berlin a kan Ukraine | Labarai | DW | 09.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron ministoci a Berlin a kan Ukraine

Ministocin sun amince za su gana da juna a ranar ta Litinin mai zuwa a babban birnin Jamus a kokarin da ake yi na kama bakin zaren warware rikicin gabashin kasar Ukraine.

Ministocin harkokin wajen Faransa da Jamus da Rasha da Ukraine za su gana a birnin Berlin fadar gwamnatin kasar Jamus a ranar Litinin inda za su tattauna kan rikicin gabashin Ukraine, da aiwatar da shirin yarjejeniyar birnin Minsk.

A wata tattaunawar zauren hadaka ta wayar tarho ministocin sun amince su gana a kokarin da ake na ganin an kama bakin warware rikicin gabashin kasar ta Ukraine kamar yadda ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana.

Minista Steinmeier Ya ce a wannan rana za su sake zama don ganin an warware matsalolin da suka dabaibaye rikicin kasar ta Ukraine. Sai dai akwai gargada da za a iya fiskanta a hanyar da ake bi wajen ganin an aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar da aka kulla ta birnin na Minsk.