Taron kungiyar Cinikaya ta Dunia WTO a Hong Kong | Labarai | DW | 14.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Taron kungiyar Cinikaya ta Dunia WTO a Hong Kong

A Hong Kong a na ci gaba da zaman taron kungiyar cinikaya ta dunia, wato WTO ko kuma OMC.

Kasashen Afrika masu noman kada da ke halartar taron, sun yi barazanar kaurace duk da wani mataki na cimma sulhu, muddun kasashen turai da Amurika, ba su amince ba, su fasa bada tallafin kudade da harakokin manoman.

A sakamkon wannan tallafi, da manoman kasashe masu attalin arziki ke samu daga gwamnatocin su, takwarorin su na Afrika na fuskantar tabarbarewar parashen kayan da su ek niomawa a cikin gida da sauran kasuwanin dunia.

Shugaban masu noman kada na Afrika, Ibarhim Mallum, ya tabatar da burin Afrikawa, shi na cimma wannan matsaya, domin kaucewa alkawuran da babu cikawa, da kasashen masu hannu da shuni, su ka dauka, a taron Cancun, na kasar Mexique, a shekara ta 2003.

A sahiyar yau, kasashen turai da Amurika, da kuma Japon, sun sake daukar sabin alkawura, na tallafawa Afrika, domin ta habaka harakokin noma, ta yada zata iya gwagwarmaya, kafada da kafada, da sauran kasashe, a kasuwanin dunia.