1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taka birki ga 'yan gudun hijira ya mamaye taron EU

Mouhamadou Awal Balarabe
February 3, 2017

Al'amura goma ne shugabannin suka sha alwashin mayar da hankali a kansu don ganin bayan masu safarar bakin haure daga Libiya zuwa kasashen Turai ta barauniyar hanya.

https://p.dw.com/p/2Wvgk
EU-Gipfel auf Malta | Gruppenbild
Shugabanni da ke halartar taron EU a MaltaHoto: Reuters/Y. Herman

Shugabannin kasashen da ke da kujera a kungiyar EU sun yanke shawarar taimaka wa Libiya yakar matsalar kwararar bakin hauren Afirka zuwa nahiyar Turai ta barauniyar hanya. Cikin wata sanarwar bayan taron da suka gudanar a Malta, shugabannin sun yi alkawarin dukufa wajen ja wa 'yan Libiya da ke safarar 'yan gudun hijira birki duk da suka da matakin ke sha daga kungiyoyin masu zaman kansu. 

Al'amura goma ne shugabannin suka sha alwashin mayar da hankali a kansu don ganin bayan masu safarar bakin haure daga Libiya zuwa kasashen Turai ta barauniyar hanya. Na farko dai shi ne taimaka wa hukumomin wannan kasa sa idanu kan iyakokinsu don hana shige da fice ta hanyoyin da ba su dace ba. Kazalika za su taimaka don a samar da sansanin da za a tsugunar da duk 'yan gudun hijirar Afirka da ke jibge a Libiya. 

Sai dai kuma tuni wasu suka fara nuna shakku kan wannan mataki saboda Libiya na fama da rikici tun shekara ta 2011. Sannan kuma gwamnatin hadin kan kasa da aka kafa a Tripoli ba ta da iko da daukacin kasar. Da ma kungiyoyin kasa da kasa tuni suka fara gargadin EU dangane da illar da ke tattare da wannan mataki. Kungiyar Save the Children ga misali ta nunar da cewar hana 'yan Afirka zuwa Turai zai jefasu musamman ma yara cikin mawuyacin hali.

EU-Gipfel auf Malta | Angela Merkel & Theresa May
Angela Merkel ta Jamus da Theresa May ta BirtaniyaHoto: Getty Images/AFP/A. Solaro

Kasashen na Turai na son dinke barakarar da ta samu tsakaninsu bayan rikicin tariyar 'yan gudun hijirar Siriya. A wancan lokaci dai kasashe irin su Poland da Hangari da Silabekiya sun ki bude kofofinsu ga 'yan gudun hijira, yayin da saura irinsu Jamus masu karfin arziki suka tarbe  su hannu biyu-biyu.

Wani batu da ke daukar hankalin shugabannin na kasashen Turai shi ne yanayin da siyasar Turai ta samu kanta a ciki tun bayan da Donald Trump ya fara shugabantar kasar Amirka. Firaministar Birtaniya Therasa May da tuni ta gana da Trump za ta yi kokarin kwantar da hankalin takwarorinta na Turai kan wajibcin biyan kudin karo-karo ga Kungiyar tsaro ta NATO idan ana son karfafa tsaro a wannan nahiya. Sai dai kuma Theresa May ba za ta halarci wani bangare na tattauna tsakanin shugabannin na EU ba.