Tababa game da babban zaben Najeriya | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 30.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Tababa game da babban zaben Najeriya

Rikicin Boko Haram da zaben da ke tafe a tarayyar Najeriya su ne batutuwan Afirka da suka fi daukar hankalin jaridun na Jamus a wannan mako.

A labarinta mai taken zaben Najeriya na cikin hadari, tashe-tashen hankula na Boko Haram na barazana ga lokacin gudanar da zaben, jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce.

Kimanin makonni biyu kafin gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya, masu ta da kayar baya na kungiyar Boko Haram na ci gaba da aikata ta'asa a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Hakan dai na barazana ga gudanar da zaben a wannan yanki, inda dubun dubatan mutane suka tsere daga rikicin yankin. Ko da yake a kwanakin bayan mai ba wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro ya yi kira da a dage lokacin gudanar da zaben da watanni uku saboda rashin samun sukunin ba da katin zabe na dindindin ga mutane miliyan 30, amma hukumar zaben kasar ta dage kan lokacin gudanar da zaben a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Zabe cikin aika-aikar 'yan bindiga

Yin zabe cikin yanayi na tarzoma inji jaridar Berliner Zeitung tana mai tababa a kan yiwuwar gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin Najeriya cikin watan Fabrairu.

Ta ce sabon katin zabe na dindindin na zaman wani abin alfahari mafi girma ga hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, domin zai hana yin duk wani magudi a zaben mai matukar muhimmanci a tarihin Najeriya da ma yankin Afirka ta Yamma gaba daya. An yi hasashen za a yi kankankan tsakanin manyan 'yan takarar neman shugabancin kasar wato shugaba mai ci Goodluck Jonathan da abokin adawa Janar Mohammad Buhari. Sai dai tashe-tashen hankula na Boko Haram da suka zama ruwan dare a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa sun fatattaki miliyoyin mazauna daga yankin, wadanda suka saura suna cikin fargaba. Jaridar ta ce a cikin wannan yanayi an kasa raba katin zaben kuma Allah kadai Ya san yawan mutanen da wannan abu ya shafa.

Aikin horas da sojojin Mali a arewacin kasar

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung ta yi tsokaci a kan horon da sojojin Jamus ke ba wa takwarorinsu na kasar Mali domin hana yankin arewacin kasar sake fadawa hannun 'yan takife masu tsattsauran ra'ayin addini.

Ta ce sojojin Jamus maza da mata su kimanin 150 ke cikin tawagar masu horaswa na kungiyar tarayyar Turai wadanda tun a bara waccan suka fara aikin horas da sojojin Mali, bayan da sojojin Faransa suka fatattaki sojojin sa kai daga arewacin kasar. Tun fara aikin yanzu haka an horas da bataliyoyi biyar wato kimanin sojoji 3000 dubarun yaki da fasahar kwance bama-bamai. Har yanzu dai 'yan tarzoma masu alaka da Al-Kaida suna kai hare-hare a arewacin Mali.

Dangantaka tsakanin Turkiya da Afirka

Kasar Turkiya na kara kyautata huldar dangantaka da kasashen Afirka, inda hatta a kasasshe irinsu Somaliya gwamnatin birnin Ankara na tafiyar da gagarumin aikin raya kasa, inji jaridar Neue Zürcher Zeitung, sannan sai ta ci gaba da cewa.

Daga shekarar 2008 Turkiya ta bude ofisohin jakadanci a kasashe 27 na Afirka, yanzu tana da wakilci a kasashe 39 na nahiyar. Yanzu haka dai kasar Turkiya ta shiga jerin manyan kasashen duniya masu ba wa kasashen Afirka tallafi, wannan taimakon ya fi tasiri a Somaliya mai fama da tashe-tashen hankula.