Sudan ta yi watsi da kudurin MDD da bukaci a tura dakaru lardin Darfur | Labarai | DW | 01.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta yi watsi da kudurin MDD da bukaci a tura dakaru lardin Darfur

Wakilan gwamnatin Sudan sun yi watsi da kudurin da kwamitin sulhu ya zartas na girke dakarun MDD a yankin Darfur mai fama da rikici dake yammacin Sudan. Wata sanarwa da hukuma ta bayar ta ce kudurin haramtacce ne kuma sabawa doka. A dangane da ci-gaba da aikata ta´asa a lardin na Darfur babban saakataren MDD Kofi Annan ya nuna damuwa game da taurin kann da gwamnatin birnin Khartoum ke nunawa. Mista Annan ya ce dakarun kasa da kasa ne kadai wadanda ba ruwansu da rikicin yankin, zasu iya sa ido don ganin an yi aiki da yarjejeniyar samar da zaman lafiya ga yankin. A jiya kwamitin sulhu ya kada kuri´ar amincewa da girke dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD wadanda zasu maye gurbin na kungiyar tarayyar Afirka a Darfur. Alkalumman da MDD sun nunar da cewa akalla mutane dubu 200 aka kashe yayin da aka tilastawa wasu miliyan biyu barin muhallinsu sakamakon fadan da ake yi a Darfur.