Sudan ta ce zata karbi ragamar kiyaye zaman lafiya a Dafur | Labarai | DW | 27.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sudan ta ce zata karbi ragamar kiyaye zaman lafiya a Dafur

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir yace mai yiwuwa ne kasar ta karbi ragamar ayyukan kiyaye zaman lafiya a yankin Dafur mai fama da rikici. Ya baiyana hakan ne a jiya a matakin kara nuna rashin amincewa da tura dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin duniya. Albashir yace Sudan a shirye take ta karbi shaánin gudanarwar kiyaye zaman lafiyar idan kungiyar gamaiyar Afrika ta sauke nauyin da aka dora mata na wannan aikin . Turjiyar da Sudan ta nuna kan tura sojojin ya haifar da rashin jituwa tsakanin gwamnatin da majalisar dinkin duniya.