Muna amfani da "Cookies" domin inganta abubuwan da muke wallafawa a intanet. Za ku iya samun karin bayani a kundin kare bayananmu.
A cikin shirin bayan Labaran Duniya, muna tafe da rahotanni ciki har da na ziyarar shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a Aljeriya. Akwai sauran rahotanni da shirye-shiryenmu da muka saba gabatar muku.
Bisa taimakon Kungiyar Tarayyar Turai, Kwararru a harkar tsaro na kasashe 10 na Sahel da Sahara na duba rawar da fararen hula za su iya takawa a yaki da ta'addanci baya ga matakan soja da ake dauka don tinkarar matsalar.
Wasu daga cikin jaridun Jamus kamar die tageszeitung da Neue Zürcher Zeitung sun yi sharhinsu ne a kan zaben shugaban kasa a Najeriya wanda ya bai wa Bola Ahmed Tinubu nasara.
A hukumance, Shugaba Emmanuel Macron na kasar Faransa ya sanar da kawo karshen aikin rundunar nan ta Barkhane da ke yaki da ta'addanci a kasar Mali.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron yana shirin sanar da janye sojojin kasarsa daga Mali tare da mayar da su wani wajen a yankin Sahel.