Shekara daya da kafuwar mulkin hadin gwiwa a Jamus
November 22, 2006Talla
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel tace gwamnatin hadin gwiwar da takewa jagoranci zata ci gaba da aiwatar da matakan garanbawul da gwamnatin ta sako a gaba.
Merkel, ta fadi hakan ne yayin da take jawabin cika shekara daya a mulki a majalisar dokoki ta Bundestag.
Bugu da kari, shugabar gwamnatin ta kuma yabi irin aikin da dakarun sojin kasar keyi a Lebanon, tare da watsi da kiran da US da NATO suka yi na fadada aikin kiyaye zaman lafiyar sojin kasar a kudancin Afghanistan.