1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhunan Jaridun Jamus akan nahiyar Afirka

Mohammad Nasiru AwalJanuary 28, 2005

Rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa yankin Darfur na Sudan shi ne batun da jaridun Jamus suka fi mayar da hankali kai.

https://p.dw.com/p/BvpV
´Yan gudun hijirar yankin Darfur
´Yan gudun hijirar yankin DarfurHoto: AP

Jama´a barkanku da warhaka. To a cikin wannan makon dai jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali akan abubuwan da ke faruwa a kasar Sudan musamman rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a yankin Darfur dake yammmacin wannan kasa. A cikin wani rahoto da ta buga, jaridar TAGESZEITUNG ta rawaito kungiyoyin ba da agaji na ketare dake wannan kasa na cewar tun makonni da dama da suka gabata dakarun gwamnati ke yi ta kai hare-hare babu kakkatawa akan fararen hula a garin Shangil Tobaya dake arewacin Darfur. Jaridar ta ce wannan dai shine karon farko da ma´aikatan ba da agajin suka shaida irin ta´asar da sojojin gwamnati ke aikatawa a Darfur. Jaridar ta ci-gaba da cewar a ran laraba da ta wuce MDD ta tabbatar da mutuwar mutane 105 sannan waus dubu 9 sun tsere daga kauyen Hamada yayin da kuma aka yi kaca-kaca da wannan kauye. Abin mamaki ne ganin yadda sojojin gwamnatin Sudan ke cin karensu babu babbaka a yankin na Darfur, amma kuma a lokaci daya kasar Amirka ke ci-gaba da hawa kujerar naki game da gurfanad da masu aikata wannan laifi a Darfur a gaban kotun duniya. A ma halin da ake ciki kusan a ce bukatar Amirka ta biya, domin wasu kasashe kamar Jamus suna goyon bayan matsayin da Amirka din ta dauka. Jaridar ta rawaito wata majiyar gwamnati a birnin Berlin na cewar ko da ya ke Jamus na tattaunawa da sauran kawayenta na KTT don cimma matsaya daya, amma duk da haka dole a daidaita da Amirka. Maimakon a gurfanad da wadanda suka aikata laifukan yaki a Darfur a gaban kotun MDD dake birnin The Hague, Amirka ta fi son a kafa wata kotun MDD ta musamman wadda zata yi zaman sauraran wannan kara. A ran daya ga watan fabrairu MDD zata yanke shawara akan wannan batu. Jaridar ta yi korafin cewar duk da tabo batun irin ta´asar da ake yi a Darfur da wani taro na musamman da babbar mashawartar MDD ta yi game da sansanin gwale-gwale na Auschwitz to amma har yanzu ba´a koyi darasi daga haka ba, hasali ma ba wani abin ku zo ku gani da gamaiyar kasa da kasa ke yi don kawo karshen wannan ta´asa a yankin na Darfur.

Har yanzu dai muna a kasar ta Sudan inda jaridar FRANFURTER ALLG. ZEITUNG ta rawaito ministar ba da taimakon raya kasa ta tarayyar Jamus Heidemarie Wieckzorek-Zeul na sukar lamirin KTT game da take-takenta a Sudan. Ministar ta yi bayyana wata yarjejeniyar ba juna hadin kai da kungiyar EU ta yi kulla da Sudan da cewa wani gurgun mataki ne. Ministar tana mai ra´ayi cewa kamata yayi a kara matsawa gwamnatin Sudan lamba don ta daina yiwa bakaken fatun yankin Darfur kisan kiyashi.

Daga Sudan bari mu leka kasar JDK inda aka kara tsunduma cikin rikicin siyasa bayan jita-jitar da aka yada game da yiwa shugaban kasa Joseph Kabila kisan gilla. Jaridar TAZ ta labarto cewar a ran talata da ta gabata mazauna Kinshasa babban birnin Kongo sun wayi gari cikin wani hali na fargaba bayan rahotannin da aka samu na kifar da gwamnati sakamakon wata musayar uta da aka yi a barikin sojin birnin. To sai dai jim kadan bayan haka shugaba Kabila ya bayyana a gaban manema labarai minda ya karyata wannan labari. To amma fa har yanzu shugaba Kabila ba iya barin fadarsa, abin da ya sanya aka dage wani taron koli na tsara lokacin gudanar da zabe, har sai cikin mako mai zuwa. To Allah Ya sawake.