1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shugaban gwamanati a sabon karni

March 17, 2022

Karkashin sabon shugaban gwamnati, tuni Jamus ta zama wata kasa ta daban. A daya bangaren kuma, hakan na faruwa ne godiya ga Shugaba Vladimir Putin da kuma kudurin Olaf Scholz.

https://p.dw.com/p/48eAT
Berlin I Shugaban Gwamnati Olaf Scholz I Taron Manema Labarai
Kwanaki 100 na shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz a gadon mulkiHoto: Odd Andersen/Pool/AP/picture alliance

Cikin sharhin da ta rubuta Michaela Küfner ta tashar DW ta ce, ya dauki Olaf Scholz kwanaki uku kacal bayan da Rasha ta afkawa Ukraine ya kifar da ginshikan manufofin ketare da tsaro na Angela Merkel da ya gaji kujerarta. A rana ta 79 bayan gwamnatin Merkel Shugaba Vladimir Putin ya sa kafa ya shure zaman lafiya a Turai. A rana ta 81 sabanin duk bayanan da suka gabata, Scholz ya tabbatar da aikewa Ukraine makaman Jamus a cikin wani sakon Twitter. Kasa da wasu sa'o'i 24 bayan haka, Scholz ya ba da sanarwar sauyin alkibla kuma ya zayyana sabuwar manufar Jamus. Saura kadan wannan ya janyo karshen siyasarsa da ma jam'iyyarsa ta SPD. Karin Euro biliyan 100 ga rundunar Bundeswehr, kuma daga yanzu akalla karin kaso biyu cikin 100 don tsaro fiye da manufar NATO!

Karin Bayani: Rudani bayan fara yakin Rasha da Ukraine

Ba 'yan jarida kadai ba hatta 'yan majalisarsa sun zare idanunsu, wasu kuma suka jefa hannayensu a kawukansu sakamakon kalaman da suka fito daga bakin shugaban gwamnatinsu da aka zaba. Ga Scholz babu gudu babu ja da baya, tun daga wannan ranar. Kusan a rana ta 50 na sabuwar gwamnati, kuri'ar jin ra'ayin jama ta daga jam'iyyar CDU mai ra'ayin mazan jiya gaba da SPD. Tsawon lokaci kalamai kalilan aka ji daga bakin shugaban gwamnati Scholz a bainar jama'a, game da barazanar yaduwar nau'in Omikron na corona tsakanin al'umma da ma muhawara kan tilasta yin rigakafin. Mai jin kunya da kamewa, tabbas bai zo a matsayin sabon shugaban gwamnati da ke da nufin sauya alkiblar abubuwa ba. Da farko dai Scholz ya yi taka tsan-tsan kan batun Rasha, shi ne ya yi tsayin daka kan diflomasiyya, har zuwa karshe. Ko da kuwa a lokacin da Hukumar Leken Asirin Amrrka ta yi gargadi kan shirin kai harin, ko kuma a kan batun.
Ko wajen ambaton bututun iskar gas na "Nord Stream 2" daga Rasha zuwa Jamus, ya yi taka tsan-tsan. Hakan ya bar tarin shakku game da amincin Jamus, a matsayin abokiyar kawance. Tambayar ita ce ko shugaban Faransa Emmanuel Macron zai zama sabon shugaban Turai, a maimakon magajin Angela Merkel? Scholz ya dauki matakin yanke hukunci ne lokacin da ya bayyana a fili cewa, duk kokarin diflomasiyya ya gaza cimma nasara. Watakila Putin ya shafe watanni yana shirin kai harin. Tare da ministar harkokin waje Annalena Baerbock shugaban gwamnatin, ya nuna cewa Jamus na son tsayawa kan wata manufa mai kima. Olaf Scholz ya shiga cikin wani sabon yanayi na siyasa sakamakon matsin lamba na al'amura, musamman daga bangaren Putin da kansa. A matsayinsa na shugaban gwamnati daga jam'iyyar da ta yi kaurin suna wajen "fahimtar Rasha," wannan wata nasara ce da kanta.

Deutsche Welle I Michaela Kuefner I TV
Michaela Kuefner ta tashar DWHoto: DW/B. Geilert

Karin Bayani: Wanene Olaf Scholz da ya ceto jam'iyyar SPD?

Sai dai sauran kasashen EU da ke da iyaka da Rasha kamar Poland da na yankin Baltic, har yanzu suna yi wa Jamus din kallon shigar burtu da wannan sabuwar fahimta. Dakatar da shigo da makamashi daga Rasha, zai kasance babbar barazana ga gwamnatin Scholz. Hakan zai yi wa yawancin al'ummar Jamus miliyan 83, wadanda har yanzu ke kokarin fahimtar abin da Putin ke ciki zafi. Galibin Jamusawan dai, suna goyan bayan shugaban gwamnatin. Amma hauhawar farashin makamashi, shi ma wani abu ne na dabam da ke damun al'umma. A yanzu dai a bayyane take cewar yakin da ake yi a Ukraine, tamkar shi ne biyan bashin da mutane ke yi ga samun 'yancin walwala da dimukuradiyyar Turai ciki har da Jamus ko da kuwa a karshe an cimma yarjejeniya da Putin. Cikin mamaki Olaf Scholz ya karbi ma'aikatan ofishin Angela Merkel na da, rahotanni da yawa sun nuna cewa Scholz ya fi Merkel gafarta kurakurai. Sai dai wannan sabon mulkin ba ya gafarta kura-kurai, kuma Scholz ba shi da niyyar yin hakan.