Sakamakon zabe a Jamus | Labarai | DW | 26.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Sakamakon zabe a Jamus

Da yammacin yau ne aka rufe rumfunan zabe daya gudana a jihohi 3 anan Jamus,wanda ke zama na farkon irinsa da hayewar Angela Merkel kejeran shugaban gwammnatin kasar,a watan nuwamban daya gabata.To sai mutane kalilan ne suka fito domin kada ckuriunsu,duk dacewa akwai kimanin mutane million 17 da suka cancanci kada kuriunsu a jihohin Baden-Wuerttenberg da Rheinland-Palatinate da Saxony-Anhalt,da aka gudanar da wannan zabe a yau.Sakamako na farko da aka samu daga Baden-Wuerttemberg na nuni dacewa jammiyar CDU ta samu kashi 45 daga cikin 100,kana SPD 25,ayayinda FDP ta samu kashi 10.5 kana the greens ta samu kashi 12 daga cikin 100 ,na adadin kuriun da aka kada.Idan har sakamakon zaben karshe ya kasance haka,to babu shakka jammiyyun CDU da FDP zasu cigaba da jagorantar jihar.

A jihar Rhein land -Palatinate kuwa Jammiyar SPD ce ke kann gaba da kashi 46.5 daga cikin 100,sai CDU data samu kashi 32,kana the greens kashi 5 bisa dari sai FDP data samu kashi 8 bisa Dari,sakamakon jihar na nuni dacewa jammiyar SPD ce zata cigaba da jan akalar wannan jiha.

A jihar Saxony-Anhalt dake gabashin jamus kuwa ,jammiyar CDU ce take gaba da kashi 37 bisa 100,ayayinda SPD tasamu 21 daga cikin 100,kana FDP ta samu kashi 7 daga cikin 100 na yawan kuriu da aka kada a zaben nayau,wannan sakamakon na nuni dacewa ,an kada gwamnatin CDU da FDP da a halin yanzu ke jan ragamar wannan jiha dake ganashin Jamus.Zaaji sakamakon karshe na zaben jihohi ukun ,a shirye shiryemmu na gaba.