Sabon yunkurin kawo karshen Boko Haram | Siyasa | DW | 11.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Sabon yunkurin kawo karshen Boko Haram

Shugabannin kasashen yankin tafkin Chadi da suka kulla kawancen yaki da Boko Haram, sun sha alwashin ganin bayan kungiyar.

A wani abin da ke zaman sabon yunkurinsu na ganin bayan kungiyar Boko Haram mai fafutuka da boma-bomai, shugbannin kasashen tafkin Chadi sun kammala wani taron wuni guda a Abuja tare da daukar matakan karfafa sabuwar rundunar hadin gwiwar kasashen mai sojoji dubbai.

Wannan ne dai karo na farko tun bayan samar da sabuwar gwamnatin tarrayar Najeriya dai, daga dukkan alamu an sake farfado da hadin kai da ma hada karfi da nufin tunkarar matsalar da ta yi sanadiyar mutuwar dubban mutane da gurgunta daukacin tattalin arziki a yankin tafkin Chad.

Makudan kudade don karfafa yaki da Boko Haram

Akasin korafi na rashin hadin kan da ta mamaye kokarin can baya dai shugabannin kasashen sun amince da samar da kudi dalar Amirka miliyan 30 domin karfafa rundunar hadin gwiwar tafkin Chadi sannan kuma da kwamandojin da za su fito daga tarrayar Najeriya da Kamaru da Chadi.

Nigeria Tschadsee Konferenz

Daga hagu zuwa dama: Sabusi Imran Abdullahi babban sakataren Hukumar tafkin Chadi, shugabanh Benin Thomas Boni Yayi, shugaba Muhammadu Buhari, sai shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

Kasashen har ila yau a sanarwar bayan taron dai sun bada tabbaci na samun taimako daga manyan kasashe masu karfin tattalin arziki na G7 domin nasarar sabon yunkurin da ya kalli Najeriyar alkawarin dalar Amirka Miliyan 100 domin samar da zaman lafiya da ma aikin kwantar da hankali da gyaran al'umma.

Matakan kuma da a fadar Muhammad Issoufou, shugaban kasar Nijar sannan kuma shugaban kasashen tafkin Chadi ya sanya sabon fatan ganin karshen matsalar a cikin gaggawa.

Farfado da fatan kawo karshen tarzoma

Nigeria Tschadsee Konferenz

Mahamadou Issoufou na Nijar da shugaban Chadi Idriss Déby da kuma na Najeriya Muhammadu Buhari

To sai dai koma wane irin tasiri fargar jajin shugabannin ke iyayi a kokari na kai karshen matsalar dai ana kallon sabo na shugabanci a Najeriyar da ma sake nunin sha'awa a bangaren turawan yamman na iya sake farfado da sabon fatan tunkarar matsalar a tunanin Maridjo Muhammad da ke zaman ministan tsaron jamhuriyar Nijar da kuma ya ce kadan ya rage su ga bayan kungiyar ta Boko Haram.

Ko bayan amfani da batun karfi na hatsi kuma shugabannin kasashen sun kuma amince da wani sabon shirin raya yankin da zai kunshi samar da aikin yi ga matasa da nufin dauke hankali daga harkar ta ta'ddanci a fadar Sunusi Imrana Abdullahi da ke zaman sakataren kungiyar kasashen tafkin Chadin da ke tsakiyar aiwatar da sabon shirin na daruruwan miliyoyi na daloli.

Sauti da bidiyo akan labarin