1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon babi a dangantaka tsakanin Jamus da Amirka

January 14, 2006
https://p.dw.com/p/BvCL

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban Amirka GWB sun kuduri aniyar inganta huldar dangantaku tsakanin Jamus da Amirka. Bayan ganawar da ta yi da shugaba Bush a fadar White House, inda suka tattauna akan batutuwan da suka samu sabani a kai, Merkel ta ce da akwai damar samar da yanayi na yarda da amincewa da juna. Ra´ayin dukkan shugabannin biyu ya zo daya a dangane da rikicin nukiliyar Iran inda suka karfafa cewar dole ne a warware wannan takaddama ta hanyar diplomasiya. Shugaban Amirka ya bayyana shirin kera makaman nukiliyar Iran da cewa babban hadari ne ga Amirka. Shugaban ya yi watsi da bukatar da Merkel ta gabatar ta rufe sansanin sojin Amirka na Guatanamo, inda take tsare da firsinonin da take zargi da laifin aikata ta´addanci.