Rundunar Libanon ta sa kafa kudancin ƙasar.
August 17, 2006Kwanaki 5, bayan lafawar yaƙi , tsakanin dakarun Isra´ila da na Hizbullahi, gwamnatin ƙasar Libanon ta fara aika dakarun ta, a kudancin ƙasar kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wutar ta yi tanadi.
Rukunin farko na sojoji, kimanin 6000 su girka sanssani a birnin Marjayoun da ke tazara kilomita 7 da iyakar Isra´ila.
Babban komandan rundunar sojojin Libanon, ya bayana cewar, nan da sa´o´i 24, sojojin za su bazuwa, a karbun iyakar da Majalisar Dinkin Dunia ta shata, tsakanin Isra´ila da Libanon.
Baki ɗaya, gwamnatin Beyruth, ta yanke shawara aika sojoji dubu 15, a yankin kudancin ƙasar.
Wannan shine karo na farko, tun bayan shekaru 40 da su ka gabata da sojojin ƙasar su ka sa ƙafa a yanki.
A nata ɓangare rundunar Isra´ila, ta miƙa fiye da rabi, na yankunan Libanon da ta mamaye, ga rundunar shiga tsakani ta Majalisar Dinkin Dunia.
A fagen diplomatia kuwa, ƙasashe da ƙungiyoyi daban-daban na ci gaba da mahaurori, a game da matakan aika rundunar sojojin, wada zata ƙara ƙarfi ga FINUL, da kuma tantance yaunin da ya rataya kan wannan runduna, kazalika, da kuɗaɗen da zata gudanar da a yuka.
A sati mai zuwa ne, a ke sa ran, Majalisar Dinkin Dunia, za ta fara aika gumen farko, na rundunar, inji Jannar Alain Pellegri, babban komandan dakarun Majalisar Dinkin Dunia a ƙasar Libanaon.
A dangane da batun, ministar harakokin wajen Isra´ila Zipi Livni, ta tantana da sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, inda ta bayanan cewar:
………………..
Ta ce: „ina kyautata zaton yanayi na gaskiya tantagarya ya bayyana a fagen diplomatia.
Aiki da ƙuduri mai lamba 1701 na tsagaita wuta, tsakanin Isara´ila da Hizbullahi, zai haifar da cenje cenje a yankin baki ɗaya, mussaman a Libanon, sannan mu duka zai haifar mana da mai ido, zuwa gaba“.
To saidai massana harakokin diplomatia, na nuna shaku a akan ɗorewa zaman lahia a wannan yanki, da ke yawan fama da riginginmu.
A game da haka, mataimakin sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia, Mark Malloch Brown cewa yayi:
„Yankin na cikin yanayi mai sarƙƙaƙiyar gaske, inda ko wa ma, na iya cinna wutar rikicin, da kan iya bazuwa dandannan.
A saboda haka, abu mafi a´ala ,shine cikin gaggawa, a samu kwance ɗamara yaƙi, sannan dakarun Libanon, da na Majalisar Ɗinkin Dunia, su kasance a yankin“.
A ɓangaren zirga zirga, kuwa, an buɗa filin saukar jiragen samar birnin Beyruth, bayan fiye da wata guda, da rundunar Isra´ila ta yi masa amen wuta.