Rasha ta maida martani kan takunkumin da aka sa mata | Labarai | DW | 19.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rasha ta maida martani kan takunkumin da aka sa mata

Rasha ta shaidawa Amirka cewar takunkumin da kasashen yamma ciki har da Amirkan suka sa mata abu ne da gwamnatin Rashan ba za su amince da shi ba.

A wata hira da ya yi da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ta wayar tarho, sa'o'i kalilan bayan da shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da ta amince da kasancewar yankin Kirimiya ya zama wani bangare na Rasha, ministan harkokin wajen Rasha Sergie Lavrov ya ce mudddin kasashen yamma ba su sauya matsayinsu kan kasarsu ba, to ba ko shakka Rasha za ta maida martani kakkausa.

Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da ake samun karin kasashen da ke yanke kauna da Moscow da ma dai bin sahun EU da Amirka wajen sanyawa Rashan takunkumi.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Zainab Mohammed Abubakar