Niger za ta mika wa Najeriya ′yan Boko Haram | Labarai | DW | 09.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Niger za ta mika wa Najeriya 'yan Boko Haram

Nijar na shirin mika wa Najeriya mutane 637 da ta kama a watanni 10 na baya-bayan nan a cikin yaki da Boko Haram da kuma take tsare da su a gidajen kurkukun kasar.

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa hukumar 'yan sandar kasar na shirin mika wa takwararta ta makobciyar kasa Najeriya wasu daruruwan mutane da ake zargi da kasancewa 'ya'yan Kungiyar Boko Haram da Nijar din ta kama a cikin watannin goma na baya-bayan nan take kuma tsare da su a gidajen kurkuku daban daban na kasar.

Yanzu haka dai wata tawagar hukumomin Najeriyar ta kai ziyara a wasu gidajen kurkuku uku na kasar ta Nijar inda tuni ta tantance wasu mutanen 457 daga cikin wadanda ake tsare da su a matsayin 'yan kasar ta Najeriya a gidajen kurkuku na birnin Yamai, Koutoukale da kuma Kollo ,yayin da ya rage a tantance wasu sauran mutanen 180.

A jimilce dai mutane 637 ne hukumar 'yan sandar kasar ta Nijar za ta mika wa takwararta ta Najeriya kamar dai yanda dama wata yarjejeniyar Kungiyar Ecowas ta tanada.