1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyar APC a Najeriya ta ci zaben cike gurbi

August 12, 2018

Hukamar zaben Najeriya ta bayyana sakamakon zaben cike gurbi na dan majalissar dattawa shiyyar Daura da ke a matsayin mahaifar Shugaban Kasar Mahammadu Bahari cikin Jihar Katsina.

https://p.dw.com/p/3325l
Nigeria Wahlen 2011 Bild 2
Hoto: DW/Gänsler

An dai fafata ne a zaben tsakanin mutum biyu daya daga jam'iyar APC mai mulki da kuma daya daga  Jam'iyar adawa ta PDP. Sai dai kuma su dukka biyun 'yan gida daya ne domin kuwa mahaifinsu daya. Shugaban hukumar zaben  Farfesa Hudu Ayuba Abdullahi ya bayyana sakamakon inda ya ce dan takara na jam'iyyar APC Ahmad Baba Keita ne ya lashe zaben da kuri'u dubu dari biyu da ashirin da hudu da dari shida da bakwai (224,607) yayin da Kabir Usman Baba na jam'iyyar PDP ya samu dubu hamsin da tara da dari bakwai da ashirin da hudu. (59,724)