Bauchi yana cikin manyan garuruwa na arewacin Najeriya kuma garin ke zama helkwatar jihar ta Bauchi.
Garin yana yankin arewa maso gabashin kasar, kuma ya kasance daya daga cikin wurare masu tasiri bisa lamuran siyasa na kasar, inda firaministan Najeriya na farko Abubakar Tafawa Balewa ya fito daga nan.