Najeriya: Ana kammala zaben gwamna a wasu jihohi | Siyasa | DW | 23.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Najeriya: Ana kammala zaben gwamna a wasu jihohi

An bude rumfunan zabe a wasu jihohin Najeriya domin kammala zaben gwamna wanda hukumar zaben kasar mai zaman kanta (INEC) ta ce bai kammalu ba a lokaicn da aka yi zaben a ranar 9 ga wannan watan.

Daga cikin jihohin da za a gudanar da wadannan zabuka akwai jihar Kano da Sokoto wadanda ke yankin arewa maso yammacin Najeriya din sai kuma jihar Bauchi da ke arewa maso gabas da kuma jihar Binuwai da ke tsakiyar kasar.

Kammala wadannan zabuka dai su ne za su bada damar sanar da wanda ya lashe zaben gwamna a wadannan jihohi. Hankali al'ummar kasar dai ya fi karkata ga jihar Kano musamman ma dai mazabar nan ta Gama da ke da yawan al'umma.

Can a jihar Bauchi kuwa hankula sun karkata kan yadda zaben zai kasance musamman ma da ya ke kusan kankankan aka yi tsakanin jam'iyyar APC da PDP a zaben da ya gudana a farkon wannan watan.